IQNA

23:07 - May 21, 2018
Lambar Labari: 3482680
Bangaren kasa da kasa, Muhammad Salah dan wasan kwalon kafa na Masar da ke wasa a Liverpool ya bayyana cewa zai yi azumia  ranar wasan karshen na kofin turai.

 

Kamfanin dillacin labaran iqna ya habarta cewa, shafin jarida Al-ahram ta kasar Masar ya bayar da rahoton cewa,a lokacin da Muhammad Salah yake amsa tambaya kan cewa ko za yi azumi a ranar wasan karshe na cin kofin nahiyar turai, ya amsa da cewa warai kuwa.

Ya ce tun da aka fara azumi a kowace rana yana yin azumi, kuma a ranar da za a buga wasan karshe na cin kofin zakarun nahiyar turai a karshen wannan mako zai yi azumi kamar yadda ya saba.

Muhammad salah dai shi ne ya lashe kyautar dan wasan da ya fi zura kwalle a wasan kasar Ingila na wannan bazarar wasanni, inda ya saka kwallaye 32.

A ranar Asabar mai zuwa za a buga wasan karshe tsakanin Liverpool da Real Madrid a birnin Kiev na kasar Ukraine.

3716520

 

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: