IQNA

23:41 - May 23, 2018
Lambar Labari: 3482685
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin Iran ta bayar da kyautar kwafi-kwafi na kur’anai da ta buga ga malaman addini na kasar Senegal a cikin wannan wata na Ramadan mai alfarma.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shugaban karamin ofishin jakadancin Iran Senegal ne ya jagoranci raba kur’anan ga manyan malaman addini na Senegal, daga ciki har da wadanda aka tarjama a cikin harshen Faransanci a kasar ta Iran.

Muhammad Jub daya daga cikin masu kula da harkokin cibiyoyin adini a Senegal, ya halarci karamin ofishin jakadancin Iran domin karbar littafn da aka ware wa babban jagoran darikar Muridiyya da jama’arsa.

Kasar Senegal dai na kyakkyawar alaka ta diflomasiyya da al’adu tare da kasar Iran, kamar yadda kuma kungiyoyin addini na kasar musamman ma na darikun sufaye suke da kyakkyawar dangantaka da kasar ta Iran.

3716935

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kwafi-kwafi na kur’anai ، dangantaka ، Senegal ، muridiyyah ، sufaye ، iqna
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: