IQNA

Ana Nuna Fim Din Tarihin Imam Ali (AS) Kai Tsaye Saliyo

23:46 - May 23, 2018
Lambar Labari: 3482687
Ana Nuna Fim Din Tarihin Imam Ali (AS) Kai Tsaye Saliyo
Bangaren kasa da kasa, tun daga lokacin da aka fara azumin watan Ramadan mai alfarma ake nuna fim din tarihin Imam Ali (AS) a kasar Saliyo.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, daga lokacin da aka fara azumin watan Ramadan mai alfarma ake nuna fim din tarihin Imam Ali (AS) a kasar Saliyo wanda ya samu karbuwa daga mutane da dama musamman ma muuslmi daga cikinsu.

A shekarar da ta gabata an rika nuna fim annabi Yusuf (AS) wanda aka tarjama a cikin harshen turanci, wanda marigayi Farajallah Salhshur dan kasar Iran ya shirya, wanda kuma an tarjama shi a cikin harsuna da dama har da harshen Hausa.

Baya ga hakan ma an nuna wasu fina-finai da ke nuna irin bakin zaluncin da yahudawan sahyuniya suke kan al’ummar musulmi na Palastine.

3716972

 

captcha