IQNA

23:42 - May 30, 2018
Lambar Labari: 3482709
Bangaren kasa da kasa, sakamakon wani harin ta’addanci da wasu ‘yan kungiyar Daesh suka kai kan ‘yan sandan Iraki a Samirra wasu daga cikinsu sun rasa rayukansu.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin kamfanin dillancin labarai na Saumariyya News cewa, sakamakon wani harin ta’addanci da wasu ‘yan kungiyar Daesh suka kai kan ‘yan sandan Iraki a Samirra wasu daga cikinsu sun rasa rayukansu yayin da kuma wasu suka jikkata.

Bayanin ya ce wasu ‘yan ta’addan wahabiyawan Daesh ne suka kaddamar da harin  akan wani shingen tsaro a garin Samirra, inda suka kasha ‘yan sanda 3 da kum ajikkata wasu 2 na daban.

3718981

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، shingen ، daesh ، Samirra
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: