Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, sakamakon kiran da wasu kasashen larabawa suka yi, babban zauren majalisar dinkin duniya zai gudanar da zaman gaggawa tare da halartar wakilan kasashe 193 kan hare-haren da haramtacciyar kasar Isra’ila ta kaddamar kan al’ummar Gaza a baya-bayan nan.
Rayad Mansur wakilin Palastine a majalisar dinkin duniya shi ne ya gabatar da takardar neman a gudanar da wannan zama, ida ya ce abin da Isra’ila ta yi kan a’ummar Gaza abin yin Allawadai ne.
Ya kara da cewa, yana yin kira ga dukkanin kasashen duniya masu ‘yancin siyasa da su yi Allawadai da abin da Isra’ila take yi kan al’ummar Palastnu na kisan kiyashi musamman kan al’ummar Gaza marassa kariya.