IQNA

Sojojin Isra’ila Sun Kashe Wani Bafalastine A Yau

13:09 - July 23, 2018
Lambar Labari: 3482841
Bangaren kasa da kasa, sojojin yahudawan Isra’ila sun kashe wani matashi bafalastine a yau da safe a sansanin Dahisha da ke Bait Lahm.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, da jiffin safiyar yau sojojin yahudawan Isra’ila sun harbe wani matashi bafalastine dan shekaru 15 da haihuwa har lahira a sansanin Dahisha da ke Bait Lahm a yankunan da yahudawa suka mamaye.

Matashin mai suna Arkan Sair Marhaz ya yi shahada ne a yau  lokacin da sojojin yahudawan suka yi harbi kan mai uwa da wabi a yankin nasu.

Baya ga hakan ma sojojin yahudawan sun kame wasu matasa biyu Muhammad Adnan Abu Ayyash da kuma wani mai suna Jamal Sar’awi, sun yi awon gaba da su zuwa wani wuri da ba a sani ba.

3732474

 

captcha