Kamfanin dillancin labaran iqna,
A ziyarar gani da ido da tawagar 'yan kwamitin kula da alakar da ke tsakanin kungiyar tarayyar Turai da Palasdinu a Majalisar Dokokin Kungiyar Tarayyar Turai ta kai zuwa kauyen Khan Ahmar da ke dauke da Palasdinawa da masu rajin kare hakkin bil-Adama na kasa da kasa da suke goyon bayan al'ummar Palasdinu a jiya Laraba.
Tawagar 'yan Majalisun Dokokin Kungiyar ta Tarayyar Turai ta jaddada cewa: Duk wani matakin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila zata dauka na rusa kauyen, yana matsayin laifin yaki ne.
Tun a ranar 12 ga wannan wata na Satumba ne kotun kolin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila ta bada izini ga sojojin haramtacciyar kasar Isra'ila kan rusa kauyen na Khun Ahmar a cikin mako guda.
Kauyen Khan Ahmar dai yana dauke ne da Palasdinawa 'yan gudun hijira da aka raba su da muhallinsu tun a shekara ta 1953, kuma a halin yanzu kauyen yana matsayin sansanin gudanar da zaman dirshen domin nuna rashin amincewa da bakar siyasar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila kan al'ummar Palasdinu.