IQNA

An Bude Taron Masana Musulmi A Kasar Turkiya

23:35 - October 15, 2018
Lambar Labari: 3483043
Bangaren kasa da kasa, A yau ne aka fara gudanar da taron kara wa juna sani na masana dagakasashen musulmi a birnin Istanbul na kasar Turkey.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Taron wanda aka yi wa take da Al’ummar Musulmi yana samun halartar masana musulmidaga bangarori daban-daban na kasashen kasashen duniya.

Sami Alarin shi ne shugaban cibiyar bincike kan lamurran addinai da al’ummomi a kasar Turkiya, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin shirya zaman taron, ya bayyana cewa babbar manufar taron ita ce kara wa juna sani kan lamurra da suka shafi duniyar musulmi a yau.

Ya ce bisa la’akari da lamurra da dama da al’ummar musulmi suke da bukatuwa zuwa gare su, akwai bukatar gudanar da taruka irin wadannan, domin jin mahangar masana daban-daban kan irin kalubalen da ke a gaban duniyar muuslmi, da kuma yadda ya kamata a fuskanci irin wannan kalubale.

Joseph Massad daga jami’ar Colombia mai nazari kan addinin musulunci, daya ne daga wadanda aka gayyata a taron domin jin mahangarsa kan musulunci.

Shi ma farid Esack daga jami’ar Johannesburg a kasar Afrika ta kudu zai gabatar da kasida kan kalubalen da musulmi suke fuskanta a kasashen da ba na musulmi ba, da kuma yadda ya kamata musulmi su nemi hakkokinsu ta hanyoyin da suka dace a irin wadannan kasashe.

3755978

 

 

 

 

captcha