IQNA

23:37 - October 19, 2018
Lambar Labari: 3483055
Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar harkokin sadarwa ta kasar Iraki ta sanar da cewa za ta samar da hanyoyi na yanar gizo kyauta ga masu ziyara.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labaran na Akhbar Iraq ya habarta cewa, ma’aikatar harkokin sadarwa ta kasar Iraki ta sanar a yau cewa ta yi tanadin hanyoyi na yanar gizo kyauta ga masu ziyarar arbaeen a wannan shekara.

Bayanin ya ce a wannan shekara masu ziyara ba za su fuskanci wata masala ta fuskar sadarwa ba, da hakan ya hada da bangaren yanar gizo da kuma layukan wayar salula.

Ma’aikatar sadarwar ta kasar Iraki ta ce za ta saki hanyoyin yanar gizo domin yin amfani da su kyauta a lokacin tarukan arbaeen, domin baki masu gudanar da wannan ziyara su amfana.

3757058

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، kyauta ، arbaeen ، Iraki
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: