IQNA

An Hana Tawagar Isra'ila Shiga Tunisia

22:57 - November 03, 2018
Lambar Labari: 3483096
Bangaren kasa da kasa, Kotun birnin Tunis fadar mulkin kasar Tunisia ta yanke hukuncin haramta wa wata tawagar Isra'ila shiga kasar, domin halartar wani taro kan addinai da za a gudanar a kasar.

Kamfanin  dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Shafin jaridar Al-shuruq ta kasar Tunisia ya bayar da rahoton cewa, sakamakon kararrakin da kungiyoyin da ke fafutukar kare hakkokin falastinawa a kasar Tunisia, domin hana tawagar Isra'ila halartar wani taron addinai da za a gudanar a kasar, kotun ta yanke hukuncinta na karshe, inda ta haramta shigowar tawagar Isra'ila a cikin kasar domin halartar taron.

Kungiyoyin sun dauki wannan matakin ne domin nuna rashin amincewarsu da abin da Isra'ila take na kisan gilla a kan al'ummar Falastinu, ba tare da duniya ta damu da hakan ba, yayin da kuma a lokaci guda ma wasu daga cikin kasashen larabawan yankin gabas ta tsakiya, suke ta hankoron ganin sun kulla alaka da Isra'ila.

A ranar 8 ga wannan wata na Nuwamba ne za a fara gudanar da taron mabiya addinai na duniya a birnin Tunis na kasar Tunisia, wanda zai samu halartar wakilai daga kasashen duniya daban-daban.

3760942

 

 

 

 

 

 

captcha