IQNA

23:58 - November 04, 2018
Lambar Labari: 3483100
Bangraen kasa da kasa, Jami'an tsaron Masar sun sanar da hallaka wasu 'yan ta'adda 19 daga cikin wadanda suka kaiwa motar Kibdawa hari.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ma'aikatar cikin gidan Masar jami'an tsaron kasar sun samu nasarar hallaka 'yan ta'adda 19 wadanda suka kaiwa motar 'yan kabilar Kibdawa hari a yankin Sohag.

A ranar juma'ar da ta gabata ce wadanda 'yan ta'adda suka kaiwa wata Bas dake dauke da 'yan kabilar Kibdawa a jahar Sohag dake kasar ta Masar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum 9 tare da jikkata wasu 14 na daban.

Jim kadan bayan kai harin, kungiyar ta'addancin nan ta daesh ta dauki alhakin kai harin.

Wannan dai bas hi ne karon farko da ake kai gare-haren ta’addanci kan mabiya addinin kirista  akasar Masar ba, kamar yadda kuma musulmi ma ba su tsira daga harin wadannan ‘yan ta’adda masu dauke da akidar wahabiyanci da kafirta muuslmi ba.

3761266

 

 

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: