IQNA

Amurka Ta Yi Fushi Domin Duniya Taki Goyon Bayanta Kan Batun Iran

22:48 - November 07, 2018
Lambar Labari: 3483107
Bangaren kasa da kasa, Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, takunkumin da Amurka ta sake kakaba wa Iran, ya kara bakanta sunan Amurka a duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, A cikin wani bayaninsa da ya yi ga al'ummar Iran, ministan harkokin wajen kasar ta Iran Muhammad Jawad Zarif ya bayyana cewa, ko shakka babu saka takunkumin da Amurka ta yi a kan a bangaren danyen man fetur, da harkokin banki da sauran harkokin kasuwanci, hakan yana nufin saka takunkumi ne a  kan al'ummar Iran kai tsaye.

Zarif ya ce, wannan mataki wanda gwamnatin Trump ta dauka ba wani abu ba ne face neman biyan bukatun wasu masu fatan ganin Iran ta durkushe, ta yadda shi kuma a shirye yake ya sayar da mutuncin Amurka da al'ummarta baki daya, matukar dai za a ba shi kudi domin yin hakan.

Ministan harkokin wajen na Iran ya ce, siyasar Trump ta mayar da Amurka saniyar ware a lamurra da dama na duniya, ta yadda hatta kasahen da suke kawayen Amurka ne a nahiyar turai, suna yin hannun riga da irin wannan salon siyasa ta Amurka a halin yanzu.

Zarif ya buga misali yadda Amurka take yin fatali da yarjeniyoyi na duniya, da hakan ya hada da yarjejeniyar dumamar yanayi ta Paris, da yarjejeniyar kasuwanci ta duniya, yarjejeniyar duniya kan shirin Iran na nukiliya da sauransu, wadanda duk gwamnatin Trump ta sa kafa ta yi fatali da su.

Baya ga haka kuma dangane da takunkumin da Amurka ta kakaba wa Iran, hakan shi ma ya kara mayar da Amurka saniyar ware, domin kuwa duniya baki daya ba ta amince da shi ba, kamar yadda kungiyar tarayyar turai gami da Rasha da China suka yi watsi da shi.

Wanda hakan ya nuna fili cewa hankoron da gwamnatin Trump take da shi da wasu 'yan tsiraru masu yi mata amshin shata ba zai yi nasara a kan kasar ta Iran ba, kuma wannan ba zai hana Iran ta ci gaba da yin aiki da dokoki na kasa da kasa ba, ko da kuwa Amurka taki yin hakan.

3761976

 

 

 

 

captcha