IQNA

Ofishin Jakadancin Iran A Najeriya Ya Kafa Kwamitin Taron Fajr

22:44 - November 14, 2018
Lambar Labari: 3483124
Bangaren kasa da kasa, ofishin jakadancin kasar Iran ya kafa wani kwamiti da zai dauki nauyin shirya tarukan cikar shekaru arba'in da samun nasarar juyin juya halin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ofishin jakadancin kasar Iranda ke birnin Abuja fadar mulkin Najeriya, ya kafa wani kwamiti da zai dauki nauyin shirya tarukan cikar shekaru arba'in da samun nasarar juyin juya halin muslunci a kasar ta Iran.

Babbar manufar hakan dai ita ce tabbatar da cewa an gudanar da taron cikin tsari da nasara kamar yadda aka saba a kowace shekara.

A shekarar bana dai ana sa ran Iran za ta gudanar da bukin cika shekaru arba'in da samun nasarar juyin juya halin muslunci fiye da dukkanin sauran shekaru da suka gabata.

Gwamnatin kasar Amurka na da shirin ganin ta kawo babban cikas ga shirin an Iran, inda jami'anta suka sha furta cewa a shekarar bana Iran ba za ta gudanar da taron zagayowar lokacin juyin juya hali ba, saboda matsalolin da za a haddasa mata na tsaro da tattalin arziki da sauransu.

3764111

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha