IQNA

'Yar Majalisar Dokokin Amurka Musulma Ta Ce Za A Iya Sayen Trump Da Kudi

20:18 - November 22, 2018
2
Lambar Labari: 3483143
Bangaren kasa da kasa, 'yar majalisar dokokin Amurka musulma Ilhan Umar ta ce Donald Trump ya tabbatarwa duniya cewa shi haja ce ta sayarwa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Ilhan Umar ta bayyana hakan ne a  shafinta na twitter, inda ta ce kalaman da shugaban Amurka Donald Trump ya yi kan batun kisan Khashoggi, ya tabbatar da cewa matsayinsa da mutuncinsa abin sayarwa ne matukar dai za a bayar da kudi.

Ta ce ba a bu ne da ya dace da shugaban kasa kamar Amurka ya fito ya bayyanawa duniya cewa shi ba zai bata alakarsa da Saudiyya ba saboda kisan Jamal Khashogi, domin kuwa Saudiyya tana bayar daruruwan biliyoyin daloli ga Amurka domin sayen makamai.

Ilhan Umar wadda ita ce 'yar majalisar dokokin Amurka musulma ta farko da za ta shiga majalisar da lullubi a kanta, ta ce za su taba amincewa da irin wannan salon siyasa na sayar da mutunci kasa da al'ummarta saboda kudi ba.

A shekaran jiya ne Donald Trump ya bayyana cewa, akwai yiwuwar ya zama Bin Salman yana da cikakkiyar masaniya kan kisan Khasohoggi, amma wannan ba zai sanya Amurka ta dauki wani mataki a kansa ba.

3766022

 

 

 

 

 

 

 

 

Wanda Aka Watsa: 2
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
Hussaini umar wali
0
0
Allah yataimakeki ilham akan makiya musulunci
Hussaini umar wali
0
0
Allah yataimakeki ilham akan makiya musulunci
captcha