IQNA

20:21 - November 22, 2018
Lambar Labari: 3483144
Kungiyar kasashen musulmi ta OIC ta sanar da cewa, kasuwanci tsakanin kasashe musulmi a cikin shekara ta 2017 ya haura dala bilyan 322.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Shafin yada labarai na Arab Alyaum ya bayar da rahoton cewa, ofishin kugiyar kasashen musulmi na OIC ya fitar da wani bayani a yau wanda a cikinsa ya bayyana cewa, kasuwanci tsakanin kasashen musulmia  2017 ya kai dala biliyan 322.2, wanda a cikin 2016 yana a dala biliyan 278.2 ne.

Bayanin ya kara da cewa, mu'amalar kasuwanci da ke tsakanin kasashen musulmi ta karfi a bangaren makamashi, ma'adanai, kayan abinci da makamantansu ne, inda a cikin shekara ta 2016 kasuwanci ya karu da kashi 18.7,a  2017 kuma ya karu da kashi 19.8.

Kasashen musulmi da suka fi tasiri ta fuskar kasuwanci a tsakanin kasashen musulmisu ne, Turkiya, Iran, Saudiyya, Malasiya, UAE, Indonesia, Masar, Oman, Iraki da kuma Pakistan, inda su ne suke da kashi 74.6 na dukkanin harkokin kasuwanci na kasashen musulmi.

3766235

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، makamashi ، karfi ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: