IQNA

Manzon MDD Na Tattaunawa Da Jami'an Gwamnatin Yemen A San'a

20:23 - November 22, 2018
Lambar Labari: 3483145
Manzon musamman na majlaisar dinkin duniya mai shiga tsakani kan rikicin Yemen na ci gaba da gudanar da tattaunawa tare da jami'an gwamnatin tseratar da kasa a San'a.

Tashar Almasira ta bayar da rahoton cewa, tun a jiya ne  Manzon na musamman na majlaisar dinkin duniya kan rikicin na Yemen Martin Griffiths yake ci gaba da gudanar da tattaunawa tare da jami'an gwamnatin tseratar da kasa da kuma bangarorin siyasa gami da shugabannin kabilun larabawan Yemen a birnin San'a fadar mulkin kasar ta Yemen.

A yau ne a aka shirya cewa Martin Griffiths zai kai ziyarar ganewa ido a garin Hudaidah da ke yammacin kasar ta Yemen, inda Saudiyya da UAE suka yi wa fararen hula da dama kisan kiyashi da kuma rusa dubban gidajen jama'a da cibiyotin kasuwanci da masallatai gami da makarantu, amma domin hana wannan ziyara, jiragen yakin UAE sun tsananta kai hare-hare a birnin a yau Alhamis, domin kawo cikas ga ziyarar ta Martin Griffiths, wanda hakan yasa ya daga ziyarar zuwa ranar Asabar mai zuwa.

3766101

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، martin Grifinths ، Yemen ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha