IQNA

Yan Ta'adda Sun Harba Makamai Masu Guba A Halab

23:47 - November 25, 2018
Lambar Labari: 3483151
Wasu gungun 'yan ta'addan takfir masu dauke da akidar wahabiyanci sun harba makamai masu dauke da guba a kan wasu unguwanni da ke cikin birnin Aleppo a nakasar Syria a daren jiya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Tashar talabijin ta Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, 'yan ta'addan sun harba makaman ne a kan unguwannin Khalidiyyah, Shari Nail, da kuma jam'iyat zahra da ke cikin birnin na Aleppo, inda utane fiye da 100 suka samu raunuka.

Rahoton ya ce, da dama daga cikin wadanda aka kai asibiti da suka hada da mata da kananan yara, suna fama da matsalar lumfashi ne, sakamakon shakar guba da ke cikin makaman da 'yan ta'addan suka harba.

Wadanan hare-hare na zuwa ne a daidai lokacin da 'yan ta'addan suke shan kashi a  hannun dakarun Syria da kuma na kungiyar Hizbullah, bayan da aka tsarkake daukacin yankunan da 'yan ta'addan suka kwace iko da su a lokutan baya a cikin lardin na Aleppo.

Tun kafin wannan lokacin da gwamnatin Rasha ta sanar da cewa, ta gano wani shiri da 'yan ta'addan suke da shi da masu daukar nauyinsu, inda suke shorin yin amfani da makamai masu guba a wasu yankuna na fararen hula, domin a  yi amfani da hakan wajen zargin sojojin Syria da yin hakan kamar dai yadda aka saba.

3766875

 

captcha