IQNA

Kira Zuwa Ga Gyaran Masallatai A Kasar Morocco

23:55 - November 28, 2018
Lambar Labari: 3483159
Bangaren kasa da kasa, ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Morocco ta yi kira zuwa ga gyaran masallatai a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Ahmad Taufiq ministan ma’aikatar kula da harkokin addini a kasar Morocco ya bayyana cewa, a halin yanzu akwai masallai kimanin 1000 da suke bukatar gyara na hakika a cikin kasar morocco.

Ministan ya ci gaba da cewa, bangarenb gwamnati da kuma kungiyoyin da suke bayar da tallafi domin gudanar da ayyukan alkhari duk suna yin iyakar kokarinsu a wannan fage.

Ya kara da cewa, a halin yanzu akwai wasu masallatai da aka gina da adadin ya kai 185, kuma 150 daga cikinsu duk kungiyoyi masu gudanar da ayyukan alkhairi ne suka gina su, wanda a cewarsa wannan babban ci gaba ne.

3768010

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha