IQNA

23:58 - November 28, 2018
Lambar Labari: 3483160
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin jami'an diflomasiya a majalisar dinkin duniya sun bayyana cewa Amurka na kokarin ganin ta kawo cikas ga kudirin kasar Yemen.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, jami'an diflomasiya a majalisar dinkin duniya sun bayyana cewa Amurka na kokarin ganin ta kawo cikas ga kudirin da aka gabatar da nufin kawo karshen rikicin kasar Yemen.

Wannan kudiri da kasar Birtaniya ta gabatar wa kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya, na da nufin ganin Saudiyya tare da kawayenta sun dakatar da hare-haren da suke kaddamarwa kan al'ummar kasar Yemen.

Haka nan kuma daftrain kudirin na da nufi bayar da dama ga al'ummar kasar da su zauna kan teburin tattaunawa domin warware matsalolinsu da kansu, ba tare da shigar wata kasa ba.

Amurka na son ganin cewa wannan daftarin bai kai labari ba, domin bayar da dama ga Saudiyya ta ci gaba da kashe fararen hula a Yemen, ita kuma ta ci gaba da sayar da makamai ga Saudiyya da kuma sauran kasashen da ke cikin kawancen.

 

3767683

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: