IQNA

23:05 - November 29, 2018
Lambar Labari: 3483162
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da gasar kur’ani mai tsarki a birnin London na kasar Birtaniya karkashin kulawar hubbaren Abbas.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a jiye ne aka kammala gudanar da gasar kur’ani mai tsarki a birnin London na kasar Birtaniya karkashin kulawar hubbaren Abbas, wanda ofishin Ayatollah Kho’I da ke Birtaniya ya dauki nauyin gasar.

Gasar dai an gudanar da ita ne a ci gaba da gudanar da taruka na tunawa da zagayowar wannan lokaci mai albarka na haihuwar manzon Allah (SAW) wanda dukkanin masoya manzon Allah suke farin ciki da zagayowar wannan lokaci.

Taron gasar kur’anin ta samu halartar baki da suka hada da wasu daga cikin jakadun kasashen musulmi da suke birnin London na kasar Birtaniya.

3768024

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: