IQNA

Tarayyar Turai Ta Ware Euro Miliyan 10 Domin Bincike Kan kur’ani

23:56 - December 20, 2018
2
Lambar Labari: 3483235
Bangaren kasa da kasa, kungiyar tarayyar turai ta ware euro miliyan 10 domin gudanar da wani bincike kan lokacin shigowar kur’ani a nahiyar turai.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na a13omk.com ya habarta cewa, kungiyar tarayyar turai ta dora wa Mercedes Garsial Arnial fitaccen masani kan harkokin tari dan kasar Spain nauyin gudanar da bincike kan lokacin shigowar kur’ani a nahiyar turai.

Kungiyar tarayyar turai ta ware euro miliyan 10 domin gudanar da wannan bincike da ta bayyana shi mai matukar muhimmanci ta fuskar tarihin nahiyar.

Garsial ya ce babbar manufar gudanar da binciken dai ita ce, sanin takamaiman lokacin da kur’ani ya fara shigowa nahiyar turai, da kuma yadda ya yi tasiri, duk kuwa da cewa nahiyar turai mazaunata ba mabiya addinin muslunci ba ne.

Ya kara da cewa, musulmi sun fara shiga cikin kasashen nahiyar turai ne bayan gama yakin duniya na biyu, bayan rushewar manyan dauloli ‘yan mulkin mallaka.

Addinin muslunci dais hi ne addinin da yafi saurin bunkasa a turai, idan aka kwatanta da sauran addinai wadanda ba na al’ummomin nahiyar ba.

3774176

 

 

 

Wanda Aka Watsa: 2
Ana Cikin Dubawa: 0
Ba A Iya Watsa Shi: 0
HAMZA AHMED INUWA
0
0
Lalle kam,aiki ya same ku kafuran banza abunda ALLAH ya tsara ba wanda ya isa ya hanata saidai kawai zamuyi muku addu'an shiryuwa ta fannin addinin Islam.
Ba A San Shi Ba
0
0
Bayyanar mahadicetakusa
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
captcha