IQNA

Rasha Ta Karyata Batun Cimma Yarjejeniya Da Ita Domin Fitar Da Iran Daga Syria

23:52 - December 22, 2018
Lambar Labari: 3483242
Gwamnatin Rasha ta karyata da'awar da Isra'ila ta yi da ke cewa, an cimma wata yarjejeniya tsakanin gwamnatin Rasha da wasu bangarori, domin fitar da Iran da Hizbullah daga Syria.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Tashar talabijin ta Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, kakakin fadar Krimilin ta kasar Rasha Dmitry Bescov ya bayyana cewa, babu gaskiya dangane da abin da Isra'ila ta fada, na cewa ta cimma matsaya tsakanin Rasha da Amurka kan ficewar sojojin Amurka daga Syria, bisa sharadin cewa Rasha za ta fitar da Iran da Hizbullah daga kasar ta Syria.

A cikin wannan makon ne Jordan ta bayar da wani bayani da ke cewa Rasha ta cimma yarjejeniya tsakaninta da Amurka, Saudiyya, Isra'ila, Masar da kuma Jordan, kan cewa Amurka za ta fice daga Syria, yayin da ita kuma Rasha za ta fitar da Iran da Hizbullah, batun da Netanyahu ya yi ta maimata shi a daren Juma'ar da ta gabata.

A ranar Laraba da ta gabata ce Donald Trump ya sanar da cewa zai janye sojojin Amurka daga kasar Syria, lamarin da wasu dga cikin 'yan majalisar dokokin kasar ta Amurka suka kalubalance shia  kansa.

3774416

 

 

 

 

 

captcha