IQNA

An Kashe ‘Yan Ta’adda 14 A Yankin Sinai Na Masar

23:57 - December 23, 2018
Lambar Labari: 3483245
Bangaren kasa da kasa, an kashe ‘yan ta’adda 14 a garin Alarish da ke arewacin kasar Masar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, a wani farmaki da sojojin kasar Masar suka kaddamar a yankin Alarish da ke cikin gudunamar Sinai a arewacin kasar Masar, an halaka ‘yan ta’adda 14.

Majiyar rundunar sojin kasar Masar ta sanar dea cewa, an kaddamar da harin ne na hadin gwiwa tsakanin sojojin kasar da kuma jami'an 'yan sanda, bayan samun bayanan sirri kan kai komon 'yan ta'adda a yankin, tare da gano maboyarsu.

Rahoton ya ce an kashe 8 daga cikin 'yan ta'addan ne bayan da aka shammace su, haka nan kuma an kashe 6 a lokacin musayar wuta tsakaninsu da jami'an tsaro.

Jami'an tsaron na Masar sun samu tarin makamai a maboyar 'yan ta'adda a garin Alarish, da suka hada da manyan bindigogi masu sarrafa kansu, da kuma sanadarai masu tarin yawa da ake hada bama-bamai da su.

3775017

 

 

 

 

captcha