IQNA

Farmakin ‘Yan sandan Yahudawan Isra’ila A Yankunan Gabar Yamma Da Kogin Jordan

19:58 - December 28, 2018
Lambar Labari: 3483258
Bangaren kasa da kasa, a yau jami’an yan sandan yahudawan Isra’ila sun kaddamar da wani samame a yankunan gabar yammma da kogin Jordan.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na Palastine yau ya bayar da rahoton cewa, da jijjifin safiyar yau jami’an yan sandan yahudawan Isra’ila sun kaddamar da wani samame a yankunan daban-daban na Palastine, inda suka yi awon gaba da wasu Falastinawa.

Rahoton ya ce, yankunan da jami’an tsaron na yahudawan sahyuniya suka kai wa farmaki sun hada da birnin Ramallah, Bait Lahm, Nablus da kuma Quds, inda suka yi awon gaba da wani addai na falastinawa.

A garin Alkhalil kuwa, jami’an tsareon yahudawan sun daura wasu kamarori a kan dukkanin hanyoyin shiga da fita garin, da nufin sanya ido domin gano wasu falastinawa da Isra’ila ke son ta kame su.

Gwamnatin kwarkwaryar cin gishin kai ta Palastine ta kirayi majalisar dinkin duniya da ta dauki mataki domin takawa Isra’ila birki kan wannan cin zarafi da take kan al’ummar Palastine, amma gwamnatin Amurka ta hana majalisar dinkin duniya yin wani katabus kan batun.

3776131

 

 

 

 

captcha