Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, kakakin majami’ar kiristocin Kibdawa akasar Masar Bolis Halim ya bayyana cewa, suna tare da shirin shugaban kasar Masar Abdulfattah Sisi, na karfafa alaka tsakanin al’ummar Masar baki daya, musamman tsakanin musulmi dakirista.
Ya ce suna goyon bayan kafa kwamiti da shugaba Sisi ya yi domin cimma wannan manufa, wanda kuma kwamitin ya hada bangarori daban-daban na al’ummar Masar, da suka hadada musulmi da kirista.
Haka nan kuma ya yi ishara da yadda wasu masu tsatsauran ra’ayi da suke da’awar jihadi suke kaddamar da hare-hare a kan kiristocia Masar, inda ya ce suna da imanin cewa masu aikata wannan aikin ba suna wakiltar musulmi ba ne.