Kamfanin dilancin labarai na iqna, Shafin yada labarai na Quds Press ya bayar da rahoton cewa, Isra'ila na shirin daukar wasu sabbin matakai na hana yin kiran sala a masallatan Falastinawa da suke kusa da matsugunnan yahudawa a birnin Quds.
Rahoton ya ce, matsugunnan yahudawan da aka gina a cikin yankunan Falastinawa na yankunan Bait Safafa, bait Hanina, da kuam Bait Makbir, wadanda dukakninsu suke a yankunan gabashin birnin Quds.
Shirin ya hada da baiwa 'yan sandan yahudawa damar shiga kowane masallaci suka ji a ana kiran salla, da su shiga su cire lasifikokin kuma su kashe wutar masallacin.
Tun a cikin shekarar da ta gabata ce dai Isra'ila ta kafa dokar hana yin kiran salla a yankunan Falastinawa da suke a kusa da matsugunnan yahudawa 'yan share wuri zauna, amma Falastinawa sun yi wasti da wannan doka, inda suke ci gaba da yin kiran salla a masallatai a duk lokutan salloli guda biyar, lamarin da yake bakanta ran yahudawan da ke a cikin yankunan.