IQNA

EU Ta Yi Allawadai Da Hukuncin Da Kotun Myanmar Ta Yanke Kan ‘yan Jaridar Reuters

22:06 - January 13, 2019
Lambar Labari: 3483312
Bangaren kasa da kasa, kungiyar tarayyar turai ta yi Allawadai da kakkausar murya dangane da hukuncin kotun kasar Myanmar a kan jaridar kamfanin dillancin labaran Reuters.

Kamfanin dillancin labaran Arakan ya bayar da rahoton cewa, bayan da kotun daukaka kara ta kasar Myanmar ta tabbatar da hukuncin daurin shekaru 7 a kan ‘yan jaridar Reuters Kyaw Soe da kuma Lone, kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya suna ci gaba da yin Allawadai da wannan hukunci.

A nata bangaren kungiyar tarayyar turai ta bayyana hukuncin da cewa abin takaici ne kuma abin tir da Allawadai ne, kuma ya kara tabbatar da cewa babu ‘yancin fadar albarkacin baki a kasar Myanmar, domin kuwa ‘yan jarida ba su da ‘yanci na gudanar da aikinsu.

A ranar Juma’a da ta gabata ce kotun daukaka kara ta kasar Myanmar ta tabbatar da hukuncin da aka yanke  akn wadannan ‘yan jarida guda biyu, sakamakon binciken da suke gudanarwa  akan kisan kiyashin da aka yi wa muuslmi ‘yan kabilar Rohingya a kasar ta Myanmar,inda kotun ta ce aikin nasu yana a matsayin fallasa asirin kasa ne.

3780740

 

 

 

 

captcha