IQNA

Sayyid Nasrullah: Babu Gaskiya Kan Jita-Jitar Da Ke Yawo Kan  Lafiyata

23:51 - January 26, 2019
Lambar Labari: 3483329
Bangaren kasa da kasa, babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya karyata jita-jitar da ake yadawa dangane da lafiyarsa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a wata zantawa da yake gudanarwa yanzu da tashar Almayadeen, babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hassan Nasrullah ya karyata jita-jitar da wasu suke yadawa kan cewa yana fama da rashin lafiya.

Sayyid Nasrullah abin ban mamaki n yadda wasu kafofin yada labarai suke ta yin magana kan cewa ba shi da lafiya, har ma wasu suna cewa ya mutu, saboda abubuwa da dama sun faru, amma bai ft ya yi magana ba, wanda hakan a cewarsu yake tabbatar da cewa akwai abin da yake faruwa dangane da lafiyarsa.

Ya ce da farko dai yana gode ma Allah, domin ba ya fama da wata rashin lafiya, bayan haka kuma shi da sauran jagororin Hizbullah sun yanke shawara kan su yi shiru dangane da surutan da Netanyahu yake ta yi, domin cimma wasu manufofinsa na siyasa, saboda haka ne aka dauki lokaci bai yi wata magana ba.

 

3784615

 

 

 

 

captcha