IQNA

Tara Ta Dala Dubu 50 Kan Cin Zarafin Wani Yaro Musulmi A Amurka

0:00 - January 27, 2019
Lambar Labari: 3483331
Bangaren kasa da kasa, sakamakon cin zarafin wani karamin yaro muuslmi a birnin Wilmington na kasar Amurka an tilasta wani wurin wanka biyan tarar dala dubu 50.

Kamfanin dillancin labaran iqna, wata makarantar musulmi a a kasar Canada ta shigar da kara, sakamakon cin zarafin wani karamin yaro muuslmi a wani wurin wanka a birnin Wilmington na jahar Delaware kasar Amurka, inda aka  tilasta wurin biyan kudi dala dubu 50 a matsayin tara.

Jawariyya han ita ce lauyar da ta shigar da kara kan wannan batu, domin kalubalantar wannan mataki na nunawa muuslmi wariya.

Ta ce ta yi farin ciki matuka da wanna nasara da suka samu, kuma hakan zai zama wani babban darasi ga duk wanda yake tunanin cin zarafin musulmi, da ya kwana da sanin cewa za su kai shi kotu domin hukunta shi.

Wannan lamari dai yana faruwa ne a cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan tun baiayn da masu tsananin kiyayya da musulmi suka karbi mulkin Amurka.

A halin yanzu dai muuslmi suna daukar matakai na fuksnatr duk cin zarafi ta hanyoyi da dama, da hakan ya hada da daukar lauyoyi domin kai lamarin gaban shari’a domin bi musu kadun hakkokinsu.

3784414

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna kamfanin dillancin labaran iqna
captcha