IQNA

23:47 - February 05, 2019
Lambar Labari: 3483350
Bangaren kasa da kasa, Iran ta ce kamfanoninta a shirye suke wajen sake gidan kasar Siriya da yaki ya daidaita.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Ministan harkokin wajen kasar ne Muhammad Jawada Zarif, ya bayyana hakan, a yayin wata ganawa da takwaransa na Siriyar, Walid Mouallem, a birnin Tehran.

Bangarorin biyu sun tattauna kan alakar dake tsakanin kasashen biyu da kuma halin da kasar ta Siriya mai fama da yaki tun cikin shekara ta dubu biyu da sha daya ke ciki.

Mista Zarif, ya bayyana wa takwaransa cewa, kamfanonin Iran a shirye suke wajen yin huldar kasuwanci da Siriya a lokacin sake gina kasar.

Idan ana tune a karshen watan Janairu da ya gabata kasashen Iran da Siriya sun cimma yarjejeniyoyi sha daya ciki harda na kasuwanci mai daurewa.

Shugaba Bashar Al'Assad na Siriya ya sha alwashin sake gina kasar ta Siriya, wanda kuma a cewarsa kamfanonin kasashen Iran da Rasha nada mihimiyar rawar da zasu taka a wannan aikin.

3787889

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، tattaunawa ، ministocin ، Iran ، Syria
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: