Kamfanin dillancin labaran iqna, a lokiacin da yake gabatar da jawabi a gaban taron tunawa da cika shekaru 40 da samun nasarar juyin juya halin muslunci a Iran a birnin Beirut, jakadan Iran a Lebanon Muhammad Jalal Firuz Niya ya bayyana cewa, bayan wadannan shekaru makomar juyin juya halin muslunci a bayyanae take ga kowa.
Taron wanda kungiyar Hizbullah ta dauki nauyin shiryawa ya samu halartar manyan ‘yan soyasa na kasar Lebanon, da kuma masana gami da malaman addini.
A cikin jawabin nasa Firuz Niya ya jinjinawa gwagwarmayar musluci dangane danasrorin da ta samu a sahyuniyawa.