Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Sheikh Ali Karawi shugaban bangaren kur’ani na hubbaren Hussaini, ya jagoranci bude cibiyar kur’ani ta Warisul anbiya a kasar da nufinn kara fadada ayyukan kur’ani mai tsarki.
Wannan na zuwa ne a ziyarar da wannan tawaga take kaiwa ne a wasu daga cikin kasashen yammacin nahiyar Afrika, da nufin ganin an kara karfafa ayyuka a bangaren kur’ni mai tsarkia dukkanin bangarori.
Haka nan kuma Karawi ya gana da wasu daga cikin malamai na kasar da suka hada da malaman mazhabar ahlul bait (AS) da suke a kasar ta Mali, wadanda suke gudanar da ayyuka a bnagaren ilmantarwa da kuma koyar da ilmominsu.
Ziyarar wannan tawaga akasar Mali tana zuwa ne bayan kammala ziyarar da wannan tawaga ta kai a kasar Burkina Faso ne, inda acan ma aka bude wata cibiyar makamanciyar wannan.