IQNA

23:58 - February 06, 2019
Lambar Labari: 3483354
Bangaren kasa da kasa, Paparoma Francis shugaban cocin batholica na duniya wanda ya ke ziyara a kasashen Latabawa ya tabbatar da cewa akwai matsalar muggan halaye na wasu malaman cocinsa dangane da lalata da yara da kuma mata.

Kamfanin dillancin labaran iqna, Paparoma Francis yana fadar haka a jiya Talata a lokacinda yake jawabi a gaban dubban masu sauraronsa a birnin Abudabi nna kasar Hadaddiyar daular laraba inda yake ziyarar aiki a can.

Paparoman ya kara da cewa akwai bukatar cocin catholika ta tashi tsaye don ganin a kauda wannan annobar wacce ta shafi fada-fada na wannan cocin a kasashen duniya da dama.

A wani bangare ya bukaci kiristoci da malaman cocin catholoca su kyautata halayensu don tabbatar da cewa an kawo karshen cin zarafin mata da yara a cikin cocin a dukkan kasashen da cocin yake da mabiya. 

A jiya ne paparoman ya kammala ziyara mai tarihi wanda ya kai birnin Abu dabi na kasar Emmerate inda ya sami dimbin taba daga kiristoci mabiya mazhabar catholica a kasar, banda haka ya gana da malaman addinin musulunci da kuma sauran kananan addinai a kasar

3788029

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: