IQNA

22:36 - February 28, 2019
Lambar Labari: 3483412
Bangaren kasa da kasa, sakamakon wani bincike ya tababtar da cewa kyamar da ake nuna wa musulmi ta karu a cikin shekara ta 2018.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kwamitin da ke sanya ido kan nuna kyama ga musulmi da ke karkashin kungiyar kasashen muslmi ya fitar da rahoton da ke cewa, kyamar da ake nuna wa musulmi ta karu a cikin shekarar da ta gabata.

Bayanin ya ce a cikin shekara ta 2017 an samu karuwar kyamar musulmi a wasu kasashen duniya idan aka kwatanta da sauran shekaru baya, amma shekara ta 2018 ta haura kowace shekara.

A cikin rahoton bayyana cewa, mafi yawan ayyukan kyamar musulmi suna faruwa ne a  cikin kasashen turai da kuma Amurka, inda ake kai hare-harea  kan masallatai da wuraren ibada da cibiyoyin ilimi na musulmi.

Yusuf Bin Ahmad Al-usaimin babban sakataren kungiyar kasashen musulmi ya bayyana rahoton da cewa bababn abin takaici ne yadda ake samun irin wannan yanayi a duniya, kuma zai mika wannan rahoto ga zaman shugabannin kasashen musulmi karo na arba’in da shida da za a gudanar.

3794153

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، gudanar ، mika ، rahoto
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: