IQNA

22:38 - February 28, 2019
Lambar Labari: 3483413
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron Isra’ila sun yi awon gaba da wasu falastinawa a wasu yankunan zirin gaza da kuma gabar yamma da kogin Jordan.

Kamfanin dillancin labaran Amasirah Net ya bayar da rahoton cewa, a yau jami’an tsaron Isra’ila sun yi awon gaba da wasu falastinawa a wasu yankunan zirin gaza da kuma gabar yamma da kogin Jordan tare da yin bincike a gidajen Falastinawa.

Rahoton ya ce jami’an tsaron yahudawan sun kame matasa falastinawa uku a yau a kauyen Deir Mush’al da ke kusa da Ramallah, haka nan kuam sun kame wasua  garuwan Safa da kuma Abu Dis.

Haka nan kuma rahoton ya kara da cewa yahudawan sun kafa wasu wuraren binciken ababen hawa na falastinawa a kusa da birnin Nablus, baya ga haka kuma suna bi gidajen Falastinawan suna kame matasa daga cikinsu.

Daga shekara ta 2018 ya zuwa Isra’ila tana tsare da falastinawa dubu 5 da 700, da suka hada da kananan yara 980, da kuma mata 175.

3794135

 

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، falastinawa ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: