IQNA

Bangaladesh Na Shirin Dauke “yan Gudun Hijirar Rihingya Dubu 103 Wani Tsibiri

23:18 - March 05, 2019
Lambar Labari: 3483426
Bangaren kasa da kasa, gwamnatin kasar Bangaladesh na shirin kwashe ‘yan gudun hijirar Rohingya dubu 103 daga sansanoninsu zuwa wani tsibiri mai nisa.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Tasjar TRT ta bayar da rahoton cewa, yanzu haka gwamnatin kasar Bangaladesh na shirin kwashe ‘yan gudun hijirar Rohingya dubu 103 daga sansanoninsu daga aka tsugunnar da su a cikin zuwa tsibirin Bhasan Char mai nisa daga sansanonin.

Gwamnatin kasar Bangaladash dai ta ce a tsibirin an tanadi komai, da hakan ya hada da wuraren zama da ruwan sha da wutar lantarki, gami da wasu kayyakin bukatar rayuwa wadanda za su wadatar da mutane akalla dubu 103.

Bayanin ya kara da cewa nan ba da jimawa ba za a fara kwashe wasu daga cikin ‘yan gudun hijirar muusmin Rohingya da suka tsere daga kasarsu ta Myamnar zuwa Bangaladash da ke makwabtaka da ita, sakamkon kisan kiyashin da ake yi musu a kasarsu..

Majalisar dinkin duniya ne ta yi gargadi kan yadda gwamnatin kasar Bangaladash ke shirin fara wanann aiki, inda ta bukaci da kada a tilasta kowa komawa tsibirin, sai dai idan a kashin kansa ya amince da hakan.

Tun a kwanakin baya gwamnatin bangaladashe ta nemi ta mayar da muuslmin Rohingya sama da miliyan daya da suke gudun hijira a cikin kasarta zuwa Myanmar, amma wasu kasashe suka bukaci da ta dakatar da yin hakan, kuma inda suka ba ta makudan kudade domin ci gaba da daukar nauyin muuslmin na kabilar Rohingya  a cikin kasarta zuwa wani lokaci.

3795190

 

 

captcha