IQNA

18:54 - March 12, 2019
Lambar Labari: 3483452
Gwamnatin kasar Amurka ta ce dole ne gwamnatin kasar Pakistan ta dauki matakan da suka dace a kan 'yan ta'adda a kasar.

Shafin yada labarai na Afhan Voice ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake ganawa da takwarasa ta kasar India a kasar Amurka, sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompoe ya bayyana cewa, Amurka tana da fahimta dangane da irin barazanar ta'addanci da India take fuskanta daga cikin kasar Pakistan.

Ya ce dole ne gwamnatin Pakistan ta dauki dukkanin mtakan da suka dace domin tunkarar wannan lamari, ko da hakan zai kai ga tattauna ne tare da 'yan ta'addan.

Pompoe ya ce Amurka za ta ci gaba da kasancewa tare da kasar India da kuma taimaka mata dangane da irin wannan barazana da take fuskanta.

A kwanakin baya dai wata kungiya da ke dauke da makamai a yankin Keshmir nba Pakistan sun kai hari kan sojojin India, inda suka kashe sojojin India 40, lamarin da ya jawo tayar da jijiyoyin wuya  atsakanin kasashen biyu.

 

3797291

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، India ، Pakistan ، Gwamnati ، Amurka
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka: