IQNA

23:39 - April 03, 2019
Lambar Labari: 3483514
Bangaren kasa da kasa, sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun harbe wani matashi bafalastine a kusa da garin Nablus.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Palastine ya bayar da rahoton cewa, a jiya sojojin yahudawan sahyuniya sun bude wutar bindiga a kan wasu matasa falastinawa biyu a kusa da garin Nablus, inda suka samu raunuka.

Daya daga cikinsu ya yi shahada a wurin, sakamakon zubar jinin da ya yi kuma sojojin yahudawan sun hana kowa isa wurinsa domin kada a ba shi wani dauki, ko ceto rayuwarsa.

Yanzu haka dai daya daga cikin matasan biyu yana raye ana kula da shi a wani asibiti.

Kafofin yada labaran Isra’ila sun ce matasan suna shirin kai hari ne akn sojojin yahudawa, amma shedun gani da idon sun tabbatar da cewa babu gaskiya a wannan rahoto, domin kuwa matasan ba su dauke da wani makami tare da su.

 

3800842

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، rahoto ، matasa ، Nablus
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: