IQNA

23:46 - April 05, 2019
Lambar Labari: 3483518
Bangaren kasa da kasa, an girmama daliban jami’oi daban-daban na kasar Iraki da suka halarci gasar kur’ani ta dalibai.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na daralquran.org ya bayar da rahoton cewa, sheikh Khairuldin Hadi, babban jami’I mai kula har kokin kur’ani na hubbaren Hussaini ya bayyana cewa, a jiya an girmama daliban jami’oi daban-daban na kasar Iraki da suka halarc gasar kur’ani ta dalibai da suka fito daga jami’oin Babul, Bagdad, Basrah, Karbala, Wasit, Musanna da sauransu.

Ya ce an bayar da kyautuka ga wadanda suka zo a matsayi na farko da na biyu da na uku.

Kyautukan sun hada da kudade da kuma litatfai gami da wasu daga cikin na’urori na zamani da za su taiamaka dalibi wajen karatunsa da kuma bincike an ilimi.

Ana gudanar da irin wannan gasa ta daliban jami’ia a kasar Iraki a kowace shekara, inda bangaren kula da harkokin kur’ani mai tsarki na hubbaren Imam Hussain da ke Karbala ne ke daukar nauyin shirya gasar.

3800973

 

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: