IQNA

Baje Kolin Kayan Aikin Rubutin Kur’ani Mai Tsarki A Kasar Aljeriya

23:55 - April 05, 2019
Lambar Labari: 3483522
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da wani baje koli na kayayyakin rubutun kur’ani mai tsarki tun daga mataki na farko a kasar Aljeriya.

Kamfanin dillancin labaran iqna, shafin yada labarai na yanar gizo na Almasa ya bayar da rahoton cewa, an fara gudanar da wani baje koli na kayayyakin rubutun kur’ani mai tsarki tun daga mataki na farko a kasar Aljeriya, wanda kananan yara ne ake nunawa wadannan abubuwa.

Bayanin ya ci gaba da cewa, an dauko yara ‘yan makaranta daga larduna daban-daban na kasar domin kawo su a wannan baje koli na kayan rubutun kur’ani mai tsarki.

Sumayya Bukhirs ita ce wadda take daukar nauyin shirya wannan baje koli, wada yake samun karbuwa daga bangarori daban na cibiyoyin kur’ani a kasar.

Ta ce ana yin amfani da kayan rubutun kur’ani ne wadanda aka gada iyaye da dakakanni, domin kuwa wasu daga cikin wadanda ake nunawa a wurin sun jima matuka.

3800921

 

captcha