IQNA

20:15 - April 09, 2019
Lambar Labari: 3483534
Majalisar kolin harkokin tsaron Jamhuriya Musulinci ta Iran, ta ayyana rundunar tsaron kasar Amurka dake yammacin Asiya a matsayin "kungiyar 'yan ta'adda".

Kamfanin dillancin labaran iqna, Majalisar wadda ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Litinin, ta ce, tana daukar gwamnatin Amurkar a matsayin mai daukar nauyin ayyukan ta'addanci, ta kuma ayyana babbar rundunar Amurkar da dakarun dake kawance da ita a yammacin Asiya, a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.

Sanarwar ta kara da cewa, Iran ta yi Allah-wadai da kakkausar murya kan yadda Amurka ta ke kokarin sanya dakarun juyin-juya halin musulunci na Iran(IRGC) a matsayin kungiyar 'yan ta'addan ketare, matakin da Iran din ta bayyana a matsayin mai hadari wadda kuma ya saba doka.

A cewar sanarwar, matakan Amurka marasa hujja da nuna son kai kan dakarun na IRGC, za su gurgunta zaman lafiya da tsaro a shiyyar, da ma duniya baki daya. Kana hakan ya keta dokokin kasa da kasa da kudurin MDD.

A jiya ne, shugaba Donald Trump na Amurka ya sanar da cewa, Amurka ta ayyana dakarun juyin-juya halin musulunci na Iran (IRGC) a matsayin kungiyar 'yan ta'adda ta ketare, matakin da zai kara dagula alakar Amurka da Iran, da ma yanayin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya.

Masana dai na ganin wannan ya bude yaki na gaba da gaba tsakanin dakarun kasashen biyu, muddin majalisar dokokin Amurka bata kalubalanci batun ba cikin kwanaki bakwai masu zuwa ba.

3802141

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: