IQNA

21:36 - April 09, 2019
Lambar Labari: 3483537
Jagoran juyin juya halin musulunci a nan Iran Aya. Sayyid Aliyul-Khaminai ya ce makarkashiyar da Amurka ke kullawa Rundunar IRGC da ma juyin  juya halin musulinci na Iran ba zai je ko ‘ina ba.

kamfanin dillancin labaran iqna, A yayin da ya gana da wani wasu gungun Sojoji na rundunar tsaron kare juyin juya halin musulinci da iyalansu, jagoran juyin juya halin Musulinci ya tabbatar da cewa dalilin da ya sanya Amurka ke nuna adawa da Dakarun IRGC saboda Dakarun sun jajirce wajen kare kasar da juyin juya halin musulinci.

Jagora ya kara da cewa Hakika Amurka da Makiya ba su iya aiwatar da wani abu ba a kan kasar Iran tsahon shekaru 40 da suka gabata ba, duk da irin karfin da suke da shi, ba rantana ba a yau da juyin juya halin musulinci da kuma tsarin musulincin ya samu karbuwa a yankin da ma Duniya baki daya.

Har ila yau jagoran ya kara da cewa duk da irin makircin da kasar Amurka da makiya ke kullawa kasar ta Iran a tsahon shekaru 40, kama daga matsin lambar siyasa, tattalin arziki, gami da farfaganda ta karya, amma kasar ta Iran ta samu ci gaba sosai wanda hakan ke tabbatar da cewa babu wata tsiya da Amurkan gami da makiya za su aiwatarwa akan jamhoriyar musulincin ta Iran.

Yayin da yake ishara kan karfin da kasar Iran din ta samu a yankin da ma Duniya baki daya, Jagora ya ce sabanin makiya da suke ganin cewa Karfi shi ne  mallakar makamin nukiliya na kare dangi, to mu tun da farko mun bayyana cewa ba ma bukatar mallakar makamin nukiliya na kare dangi domin ya sabawa Addininmu, a yau Kasar Iran ita ce Duniyar musulmi ta sanyawa ido, kuma wannan matsayi da Iran din ta samu sakamakon juriya, sadaukarwa da basirar Al’ummar Iran ne.

3802273

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: