IQNA

23:52 - April 11, 2019
Lambar Labari: 3483540
Ana ci gaba da zaman dar-dar a kasar Sudan bayan da kai da komowar sojojin kasar a manyan cibiyoyin gwmanatin kasar ke karuwa.

Kamfanin dillancin iqna, rahotannin da suke fitowa daga birnin Khartum sun ce tun da tsakiyar daren jiya ne sojoji da motocinsu masu sulke suka kame mafi yawancin cibiyoyin gwmanati da suka hada da gidan Radiyo da kuma fadar shugaban kasa.

Wata majiyar ta tabbatar da cewa; Sojoji sun yi wa shugaban Umar Hassan al-Bashir daurin talala, kamar kuma yadda su ka kame manyan jami’an gwamnati na bayan da na yanzu.

Gidajen Radiyo da Talabijin din kasar Sudan sun dakatar da watsa duk wasu shirye-shirye idan ba badujalar sojoji ba.

Wannan matakin na sojojin kasar ya biyo bayan watanni 4 da al’ummar kasar su ka dauka suna gudanar da Zanga-zangar kira ga shugaban kasar da ya yi murabus.

 

3802819

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، sudan
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: