IQNA

22:17 - April 14, 2019
Lambar Labari: 3483546
Bangaren kasa da kasa, jam’iyyar Umma mai adawa  akasar Sudan ta bukaci da a sako dukkanin mambobinta da ake tsare da sua  cikin gidajen kaso a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, tashar talabijin ta Russia Today ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ta fitar a yau, jam’iyyar Umma ta bukaci mahukuntan sojin da suke tsare da mambobinta da su gaggauta sakinsu ba tare da wani bata lokaci ba.

Bayanin ya ci gaba da cewa, abinj da sojin kasar suka yin a darewa kan kujerar shugabancin kasar ya sanawa dukaknin kaidoji da dokoki na kasar, kuma dole ne su gaggauta mulki ga hannun farar hula domin su mulki kansu.

Daga karshe jam’iyyar ta bayyana cewa babban abin da al’ummar kasar suke bukata shin e mulki na dimukradiyya wanada zai ginu a kan abin da jama’a suke bukata kuma suka zaba ma kansu.

3803423

 

 

 

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، sudan ، dimukradiyya
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: