IQNA

22:54 - April 15, 2019
Lambar Labari: 3483548
Bangaren kasa da kasa, bangarorin siyasa da na addini da dama a kasar Amurka sun nuna goyon bayansu ga Ilhan Omar kan cin zarafin da Trump ya yi a kanta.

Kamfanin dillancin labaran iqna, kamfanin dillancin labaran Anatoli ya bayar da rahoton cewa, a cikin ‘yan kwanakin nan Donald Trump tare da kungiyoyin yahudawan Amurka suna ta hankoron ganin sun bata sunan ‘yar majalisar dokokin kasar ta Amurka musulma Ilhan Omar.

Sakamakon irin sukar da Trump da kungiyoyin yahudawa suke yi wa Ilhan Omar, wasu daga cikin kungiyoyin mabiya addinai daban-daban da kuma ‘yan siyasa a kasar ta Amurka sun fito sun nuna cikakken goyon bayansu a gare ta.

Wata babbar kungiyar yahudawa mai adawa da Isra’ila (Jewish Voice for Peace) ta fitar da wata sanarwa, ind a ciki ta kirayi dukkanin magoya bayanta da suka su bayar da kariya ga Ilhan Omar, baya ga haka kuma kungiyar ta jaddada goyon bayanta ga dukkanin abin da Ilhan take fada kan zalunci da kama karya irin na yahudawan Isra’ila, inda kungiyar ta ce gwamnatin Isra’ila bat a wakilatr dukkanin yahudawa.

Shi ma a nasa bangaren mark Tokano dan majalisar dokokin Amurka daga jahar California ya bayyana cewa, kalaman batuncin da Trump ya yi kan Ilhan Omar saboda ta musulma babban abin kunya ne ga dukkanin al’ummar Amurka.

A nasa bangaren shi ma Jimmy Carter tsohon shugaban kasar ta Amurka, ya bayyana sukar Ilhan Omar saboda addininta  a matsayin abin day a sabawa doka a kasar Amurka, inda ya ce kowane mutum yana hakkin ya yi addininsa a cikin Amurka, haka nan kuma Jimma Carter ya soki wata kungiyar yahudawa waddata c eta dorawa Ihan Omar takunkumi.

 

3803673

 

 

 

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: