IQNA

Saudiyya Ta Kashe ‘Yan Shi’a 33 Saboda Dalilan Siyasa

20:20 - April 25, 2019
Lambar Labari: 3483577
Kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa, da suka hada da Amnesty International da Human Rights Watch sun zargi gwamnatin Saudiyya da zartar da hukuncin kisa saboda dalilai na siyasa.

Kamfanin dillancin labaran iqna, a cikin bayanan da suka fitar, kungiyoyin kare hakkin bil adama sun bayyana kisan da masarautar iyalan Saud ta yi wa wasu mutane 37 a ranar Talata da ta gabata da cewa lamari ne mai daga hankali matuka.

Bayanin ya ce 33 daga cikin dukkaninsu ‘yan shi’a ne wadanda aka kama saboda dalilai na siyasa, daga cikinsu har da kananan yara, wadanda lafinsu shi ne sun shiga zanga-zangar nuan adawa da salon mulkin mulukiya na kasar, inda dukkansu aka sare musu kawuna a ranar Talata da ta gabata.

A nata bangaren kungiyar tarayyar turai a ta bakin bababn kwamishinan kungiyar kan hakkokin bil adama Michelle Bachelet, ta bayyana kisan wadannan fararen hula da saudiyya ta yi saboda dalilai na siyasa da cewa, hakan ya yi hannun riga da dukkanin dokoki da kaidoji na duniya.

Yanzu haka masarautar Al Saud na shirin sake fille kawunan wasu daga suka hada har da masu rajin kare hakkokin bil adama a kasar, da kuma wasu mata masu fafutar kare hakkokin mata a kasar, duk bisa tuhuma ta ayyukan ta’addanci.

3806322

 

 

captcha