Kamfanin dillancin labaran iqna, shugaba Rauhani ya bayyana hakan ne a lokacin da yake gudanar da wani ran gadi a wata babbabr madatsar ruwa da aka kaddamar a lardin Keramnshah da ke yammacin kasar ta Iran.
Ya ce ko shakka babu takunkuman Amurka suna da nasu tasiri, amma kuma hakan ba zai iya hana Iran sayar da man nata ba a duniya, kuma akwai matakai da kasar ta Iran take dauka a kan wannan lamari, wanda tabbas zai cutar da ita kanta kasar ta Amurka.
Rauhani ya ce al’ummar kasar Iran sun dogara da kansu ne a mafi yawan abubuwan da suke da buktuwa a gare su, wanda kuma hakan sakamako ne na takunkuman Amurka na tsawon shekaru arba’in, kuma a wannan karon ma, wadannan takunkumai babu abin da za su karawa kasarsa zai dogaro da kanta.