IQNA

1:59 - May 05, 2019
Lambar Labari: 3483606
Bangaren kasa da kasa, an cimma yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin Iran da Habasha kan taimaka ma mata musulmi.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Malam Sartu Shmasuddin babbar darakta da ta cibiyar mata musulmi ta bayyana cewa, an cimma yarjejeniya tsakanin Iran da Habasha kan taimaka ma mata musulmi da suke kasar a bangarori daban-daban da suke bukatar taimako.

Hassan Haidari shugaban karamin ofishin jakadancin Iran a kasar Habashaba ya bayyana cewa, akwai kyakkyawar fahimta tsakanin Iran da sauran dukkanin bangarorin da cibiyoyin musulmi a kasar Habasha.

Haka nan ita ma ta ce a halin yanz mata da dama suna gudanar da ayyuka a bangarori daban-daban naci gaban su, da kuma samar da hanyoyi na bunkasa ilmi na addinin musulunci.

Haidari ya kara da cewa, Irana  shirye ta bayar da dukkanin abubuwan da ake bukata ta fuskacin koyarwa ga musulmi mata a kasar Habasha, tare da wadata cibiyoyinsu da kayan aiki.

 

3808686

 

Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: