IQNA

19:56 - May 07, 2019
Lambar Labari: 3483616
'Yan sandan Sri Lanka sun sanar da cewa sun samu nasarar kame dukkanin wadanda suke da hannu a hare-haren da yi ajalin mutane 257 a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar talabijin ta Aljazeera ta bayar da rahoton cewa, a yau  Chandana Wickramaratne babban sufeton ‘yan sanda na kasar Sri Lanka ya bayyana cewa, sun samu nasarar kame ko kuma kashe dukkanin wadanda suke da hannu a hare-haren ta’addancin da aka kai a kasar a ranar 21 ga watan Afirilun da ya gabata.

Ya ce an kai samame a maboyar ‘yan ta’addan a wurare daban-daban, kuma an samu tarin makamai da abubuwan harhada bama-bamai da wasu abubuwa masu tarwatsewa.

Haka nan kuma ya kara da cewa, an dauki kwararan matakan tsaro a dukkanin wurare taruwar jama’a, musamman a makarantu, inda ‘yan ta’addan ke barazanar za su kai hare-hare.

A ranar 221 ga watan Afirilun da ya gabata ne dai aka kai hare-haren ta’addanci, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 257, da kuma jikkatar wasu 500 na daban.

3809637

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، wadanda ، ، ،
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: