IQNA

22:34 - May 09, 2019
Lambar Labari: 3483624
Kungiyoyi masu tsananin kiyayya da addinin musulunci a kasar Amurka, sun samu taimakon da ya kai dala miliyan 125 a tsakanin shekarun 2014 zuwa 2016.

Kafanin dillancin labaran iqna, Jaridar Daily Sabah ta bayar da rahoton cewa, majalisar musulmin kasar Amurka ta fitar da wani bayani dangane da sakamakon wani bincike da aka gudanar kan kungiyoyin masu kyamar muuslmi a kasar, da ke nnuna yadda kungiyoyin suke samun tallafin kudade daga kungiyoyi masu tara taimako domin ayyukan alhairi a kasar.

Sakamakon binciken ya nuna cewa, cibiyoyi 1096 da kuma kungiyoyi 39 ne suke taimaka masu tsananin kiyayya da musulmi a kasar Amurka da makudan kudade.

Rahoton ya ce jimillar kudaden da kungiyoyi masu adawa da musulunci suka samu a cikin wannan lokacin da aka ambata ya kai dala biliyan 1.5, wanda aka yi amfani da su wajen bayar da cin hanci ga wasu kafofin yada labarai, da bangarorin ‘yan siyasa, da ‘yan sanda da kuma kungiyoyin yahudawa masu tasiri, domin mara baya yunkurin wadannan kungiyoyi na nuna adawa ga musulmi da musulunci a kasar.

Daga cikin fitattun kungiyoyin da suka tara gagarumin taimako ga masu tsananin kiyayya da musulmi a  Amurka, a kwai kungiyoyin Middle East Forum, da kuma ACT for America.

3809913

 

 

Abubuwan Da Ya Shafa: iqna ، kamfanin dillancin labaran iqna ، musulmi ، Amurka ، tasiri
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: